User:HausaDictionary/Quran/51
Appearance
- Wazzariyati zarwa
- By those [winds] scattering [dust] dispersing <> Inã rantsuwa da iskõki mãsu shẽkar abũbuwa, shẽƙẽwa. = Da iskoki masu naushi. --Qur'an 51:1
- Falhamilati wiqra
- And those [clouds] carrying a load [of water] <> Sa'an nan da girãgizai mãsu ɗaukar nauyi (na ruwa)= Sa'an nan da giragizai masu daukan ruwa--Qur'an 51:2
- Faljariyati yusra
- And those [ships] sailing with ease <> Sa'an nan da jirãge mãsu gudãna (a kan ruwa) da sauƙi= Masu gudanar da tanadi--Qur'an 51:3
- Fal muqassimati amra
- And those [angels] apportioning [each] matter, <> Sa'an nan da Malã'iku mãsu rabon al'amari (bisa umurnin Allah)= Suna masu rabonsu a bisa umurni--Qur'an 51:4
- Innama tu'aduna lasawdiq
- Indeed, what you are promised is true<> Lalle abin da ake yi muku alkawari (da zuwansa), haƙĩƙa gaskiya ne= Lalle abin da aka yi maku alkawari da zuwansa, gaskiya ne--Qur'an 51:5
- Wa'innaddeena la waq'e
- And indeed, the recompense is to occur<> Kuma lalle sakamako (ga ayyukanku), haƙĩƙa, mai aukuwa ne = Haqiqa ranaran sakamako mai aukuwa ne --Qur'an 51:6
- Wassamaaa izatul hubuk
- By the heaven containing pathways, <> Inã rantsuwa da samã ma'abũciyar hanyõyi (na tafiyar taurãri da sautin rediyo)= Duk da cewan an halitta sama babu aibi--Qur'an 51:7
- Innakum lafee qawlin mukhtalif
- Indeed, you are in differing speech<> Lalle kũ, haƙĩƙa, kunã cikin magana mai sãɓa wa juna (game da Alƙur'ani)= Kuna ta husuma game da gaskiya--Qur'an 51:8
- You'faku anhum man ufik
- Deluded away from the Qur'an is he who is deluded<> Anã karkatar da wanda aka jũyar (daga gaskiya)= Masu karkatawa daga gaskiya su ne masu karkatawa--Qur'an 51:9
- Qutila khaurasoon
- Destroyed are the falsifiers <> An la'ani mãsu ƙiri-faɗi= An la'ani ma-qaryata--Qur'an 51:10
- Allazinahum fee jamratoon sahoon
- Who are within a flood [of confusion] and heedless<> Waɗanda suke shagala a cikin zurfin jãhilci= Wadanda suka shagala a cikin zurfin jahilci--Qur'an 51:11
- Yas aloona aiyyana yaumuddeen
- They ask, "When is the Day of Recompense?" <> Sunã tambaya: "Yaushe ne rãnar sakamako zã ta auku?" = Suna qalubalantar tsayiwar ranar sakamako--Qur'an 51:12
- Yau mahum alannari youftanoon
- [It is] the Day they will be tormented over the Fire <> Ranar da suke a kan wuta anã fitinar su= Ranar da za gabatar da su ga wuta--Qur'an 51:13
- Zuqu fitnatakum hazallazi kuntumbihi tasta'jiloon
- [And will be told], "Taste your tormentThis is that for which you were impatient." <> (A ce musu): "Ku ɗanɗani fitinarku, wannan shĩ ne abin da kuka kasance kunã nẽman zuwansa da gaggãwa." = (A ce masu): "Ku dandani azaba; wannan shi ne abin da, da kuke qalubalanta--Qur'an 51:14
- Innal muttaqina fee jannatin wa'uyoon
- Indeed, the righteous will be among gardens and springs, <> Lalle mãsu taƙawa, sunã a cikin lambunan itãce da marẽmari= Masu taqawa su ne suka cancanci lambuna da maremari--Qur'an 51:15
- Accepting what their Lord has given themIndeed, they were before that doers of good<> Sunã mãsu dĩbar abin da Ubangijinsu Ya bã suLalle sũ, sun kasance mãsu kyautatãwa a gabãnin haka (a dũniya)= Za su debi ladar Ubangijinsu, saboda da sun kasance masu kyautatawa a gabanin haka--Qur'an 51:16
- They used to sleep but little of the night, <> Sun kasance a lõkaci kaɗan na dare suke yin barci= Ba safai ba suke yin barcin dare dukanta ba--Qur'an 51:17
- And in the hours before dawn they would ask forgiveness, <> Kuma a lõkutan asuba sunã ta yin istigfãri= Kuma a lokutan asuba suna yin istigfari--Qur'an 51:18
- And from their properties was [given] the right of the [needy] petitioner and the deprived<> Kuma a cikin dũkiyarsu akwai hakki ga (matalauci) mai rõƙo da wanda aka hana wa rõƙo= Kaso a cikin dukiyarsu akwai hakki da suka ajiye saboda masu roqo da matalauta--Qur'an 51:19
- And on the earth are signs for the certain [in faith] <> Kuma a cikin ƙasã akwai ãyõyi ga mãsu yaƙĩni= Kuma a cikin qasa akwai ayõyi ga masu yaqini--Qur'an 51:20
- And in yourselvesThen will you not see? <> Kuma a cikin rãyukanku (akwai ãyõyi)To, bã zã ku dũbã ba? = Da a cikin rayukanku; za ku iya gani? --Qur'an 51:21
- And in the heaven is your provision and whatever you are promised<> Kuma a cikin sama arzikinku (yake fitõwa) da abin da ake yi muku alkawari= A cikin sama arzikinku ke fitowa, da duk abin da ake yi maku alkawari--Qur'an 51:22
- Then by the Lord of the heaven and earth, indeed, it is truth - just as [sure as] it is that you are speaking<> To, kuma Ina rantsuwa da Ubangijin sama da ƙasã, lalle shĩ (abin da ake yi muku alkawari), haƙĩƙa gaskiya ne, kamar abin da kuka zamo kunã karantãwa na magana, = To, kuma Ina rantsuwa da Ubangijin sama da qasa, wannan gaskiya ne, kamar tabbacin gaskiya cewa kuna magana--Qur'an 51:23
- Has there reached you the story of the honored guests of Abraham? - <> Shin, lãbãrin Bãƙin Ibrãhĩm, waɗanda aka girmama, ya zo maka? = Shin, labarin baqinIbrahim, wadanda aka girmama, ya zo maka? --Qur'an 51:24
- When they entered upon him and said, "[We greet you with] peace." He answered, "[And upon you] peace, [you are] a people unknown<> A lõkacin da suka shiga gare shi, sai suka yi sallama; ya ce "Aminci ya tabbata a gare ku, mutãne bãƙi!" = Sa’ad da suka ziyarce shi, suka yi “sallama” ya ce "Salam gare ku mutane baqi!" --Qur'an 51:25
- Then he went to his family and came with a fat [roasted] calf <> Sai ya jũya zuwa ga iyãlinsa, sa'an nan ya zo da maraƙi tutturna, = Sai ya sa iyalinsa ta shirya wata maraqi tutturna--Qur'an 51:26
- And placed it near them; he said, "Will you not eat?" <> Sai ya kusantar da shi zuwa gare su, ya ce: "Bã zã ku ci ba?" = Sa’ad day ya basu, ya ce, "Ba za ku ci ba?" --Qur'an 51:27
- And he felt from them apprehensionThey said, "Fear not," and gave him good tidings of a learned boy<> Sai ya ji tsõro daga gare suSuka ce: "Kada kaji tsõro." Kuma suka yi masa bushãra da (haihuwar) wani yaro mai ilmi= Sai tsoro ya kama shi game da suSuka ce, "Kada kaji tsoro," sai suka yi masa bishara da (haihuwar) yaro mai ilmi--Qur'an 51:28
- And his wife approached with a cry [of alarm] and struck her face and said, "[I am] a barren old woman!" <> Sai matarsa ta fuskanta cikin ƙyallõwa, har ta mari fuskarta kuma ta ce: "Tsõhuwa bakarãriya (zã ta haihu)!" = Sai matarsa ta yi mamakiTana kallon takureren fuskarta: ta ce, "Ni tsohuwa ce bakarariya." --Qur'an 51:29
- They said, "Thus has said your Lord; indeed, He is the Wise, the Knowing." <> Suka ce: "Kamar haka Ubangijinki Ya faɗaLalle Shĩ, Shĩ ne Mai hikima, Mai ilmi." = Suka ce, "Kamar haka Ubangijinki Ya faɗaShi ne Mafi hikimah, Mai ilmi." --Qur'an 51:30
- [ Abraham ] said, "Then what is your business [ here ], O messengers?" <> ( Ibrãĩm) ya ce: "To mẽne ne babban al'almarinku, yã kũ Manzanni!" = (Ibrahim) ya ce, "To ina kuka nufa, ya ku manzanni?" --Qur'an 51:31
- Waalththariyati tharwan
- Faalhamilati wiqran
- Faaljariyati yusran
- Faalmuqassimati amran
- Innama tooAAadoona lasadiqun
- Wainna alddeena lawaqiAAun
- Waalssamai thati alhubuki
- Innakum lafee qawlin mukhtalifin
- Yufaku AAanhu man ofika
- Qutila alkharrasoona
- Allatheena hum fee ghamratin sahoona
- Yasaloona ayyana yawmu alddeeni
- Yawma hum AAala alnnari yuftanoona
- Thooqoo fitnatakum hatha allathee kuntum bihi tastaAAjiloona
- Inna almuttaqeena fee jannatin waAAuyoonin
- Akhitheena ma atahum rabbuhum innahum kanoo qabla thalika muhsineena
- Kanoo qaleelan mina allayli ma yahjaAAoona
- Wabialashari hum yastaghfiroona
- Wafee amwalihim haqqun lilssaili waalmahroomi
- Wafee alardi ayatun lilmooqineena